WATA Hajiya daga Nigeria Tahaihu A Makka

Wata Hajiya daga Nijeriya ta haihu a Makka

Wata daga cikin alhazai maniyyata aikin hajjin bana 'yar Nijeriya da aka sakaye sunanta ta haihu a birnin  Makkah.

Shugaban kungiyar likitocin NAHCON, Dakta Usman Galadima, ne ya bayyana hakan jiya a garin Makkah yayin da yake zantawa da wasu ‘yan jarida a kasar ta Saudiyya.

Mahajjaciyar, wacce ke dauke da juna biyu na watanni bakwai, an kwantar da ita a daya daga cikin asibitocin Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) da ke Makkah inda kungiyar likitocin Nijeriya ta taimaka mata wajen haihuwa.

Daga:Mas'ud Ibrahim k'koshi