TAWAGAR MU (OUR TEAM)
Marubuta da Editocin da ke Bada Gudunmawa a Fidelity Hausa
A Fidelity Hausa, muna alfahari da tawagar ƙwararru, masu jajircewa, da kuma ƙwarewa waɗanda ke sadaukar da kansu wajen kawo labarai masu inganci da gaskiya. Kowane memba a cikin tawagar mu yana da gagarumar gudunmawa wajen cimma burin mu na "Gaskiya Da Gaskiya".
Najib Hussaini Ahmad
(ABU MUS'AB)
Chief Executive Editor, Fidelity Hausa kuma Mamallakin Jaridar
Najib Hussaini Ahmad (ABU MUS'AB) ƙwararre ne a fannonin fasaha da aikin jarida. Yana da gogewa a bangaren Technology, ciki har da Graphic Design, Computer Networking, Cyber Security, Video Editing da Sound Editing.
Ya yi karatu a fannonin Computer daban-daban, sannan yana da ƙwarewa a aikin jarida. Ya yi Basic Mass Communication, kuma ya samu horo daga wasu manyan kafafen sadarwa da hukumomi kamar Reuters, Meta da Arewa Updates. Haka kuma yana da takardun shaidar kammala karatu (Certificates) a fannin aikin jarida.
Aliyu Bala Gerengi
Senior Reporter, Fidelity Hausa
Aliyu Bala Gerengi babban mai rahoto ne a Fidelity Hausa, wanda ke aiki a matsayin Reporter, Mai Gabatar da Shirye-shirye da Mai Tattaunawa (Interviewer).
Shi ɗan jarida ne da ke zaune a Jihar Gombe, Arewa Maso Gabashin Najeriya. Yana aiki a matsayin mai gabatar da labarai, mai fassara da kuma mai gabatar da shirye-shirye a gidajen rediyo da talabijin na jihar Gombe wato GMC Radio da GMTV.
Haka kuma shi ne wakilin Bakandamiya TV a Jihar Gombe, wakilin Fidelity Hausa Online Newspaper, sannan kuma wakilin Global Talk America a Jihar Gombe.
Mudassir Saleh Labaran
Ɗan jarida ne, mai shirya rahotanni kuma mai gyaran sauti (Sound Editor) a Fidelity Hausa Online Newspaper.
Yana gudanar da aikin rahoto daga Jihar Kano, Najeriya, inda yake tattara bayanai, rubuta labarai, gudanar da hirarraki da shirya rahotannin rediyo da na kafafen sada zumunta.
A halin yanzu, Mudassir yana aiki da GCMX Radio/TV Kano a matsayin mai rahoto, bayan ya fara aikin jarida a Fidelity Hausa Online Newspaper. Yana da ƙwarewa wajen samar da ingantattun rahotanni musamman kan batutuwan da suka shafi rayuwar al’umma, fasaha, ci gaban ƙasa da sauran muhimman al’amuran yau da kullum.
Baya ga aikin jarida, Mudassir yana da ƙwarewa a fannin sadarwa da tsaron bayanan intanet (Cybersecurity). Ya mallaki Professional Diploma in Mass Communication, Professional Diploma in Cybersecurity, da kuma takardar shaidar Certiport IT Specialist – Cybersecurity, wanda suka ƙara masa ƙwarewa a fannin fasaha da harkokin kafafen yaɗa labarai.
Aishatu Umar Muhammad
Mai Karanta Labarai kuma Mai Gabatar da Shirye-shirye, Fidelity Hausa
Aishatu Umar Muhammad ta samu horo a bangaren Mass Communication a Fidelity Hausa, sannan ta yi karatu ta hanyar Online Class na MAP.
Ita ce mai karanta labarai a Fidelity Hausa, kuma tana gabatar da shirye-shirye da tattaunawa da mutane. Ta taba aiki da MAP Radio Online, sannan ta samu gogewar aiki a Progress Radio Gombe.
Umar Ya’u Abdullahi
Reporter, Fidelity Hausa
Umar Ya’u Abdullahi mai rahoto ne a Fidelity Hausa. Yana da Certificate a Basic Mass Communication, sannan yana da kwarewa a fannonin Graphic Design da Video Editing.
Habiba Ahmad Diyee
Wakiliyar Fidelity Hausa a Jihar Bauchi
Habiba Ahmad Diyee ita ce wakiliyar Fidelity Hausa a Jihar Bauchi. Haka kuma ita ce wakiliyar shirin Birgami Labari na gidan rediyo GLO FM Bauchi, inda ta shafe sama da shekaru biyu tana aiki tare da su.
Haka kuma ma’aikaciyace a Bauchi A Yau TV, inda ta fara aiki a ranar 11/07/2024 kuma har yanzu tana ci gaba da aiki tare da su.
Umar Yahya Shuaibu
Reporter, Fidelity Hausa
Umar Yahya Shuaibu mai rahoto ne a Fidelity Hausa. Ya yi Professional Diploma sannan ya yi Higher Diploma in Computer.
Yana da kwarewa a fannonin Video Coverage da Graphic Design, tare da sauran ayyukan fasaha da suka shafi kafafen sadarwa.