Kungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), Majalisar Jihar Gombe, ta miƙa saƙon taya murna da girmamawa ga Farfesa Umaru A. Pate bisa nasarar kammala wa’adinsa a matsayin Mataimakin Shugaban Jami’ar Tarayya ta Kashere, Jihar Gombe.
A cikin wata sanarwa da Shugaban Majalisar, Faruk Mu’azu Gombe, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta bayyana cewa jagorancin Farfesa Pate ya kasance abin koyi, mai cike da hangen nesa, kwarewa da jajircewa wajen bunƙasa ilimi da ci gaban cibiyoyin ilimi a Najeriya.
Sanarwar ta ce, a tsawon wa’adinsa, jami’ar ta samu gagarumin sauyi a fannoni da dama, ciki har da faɗaɗa gine-gine, ƙaddamar da sabbin shirye-shiryen karatu, ƙarfafa bincike da kuma inganta tsarin gudanarwa.
Ta kara da cewa wadannan matakai sun taimaka wajen ɗaga darajar jami’ar a matsayin daya daga cikin cibiyoyin ilimi masu tasiri a yankin Arewa maso Gabas da ma kasa baki ɗaya.
Majalisar ta jaddada cewa wa’adin Farfesa Pate ya kasance mai cike da gaskiya, riƙon amana da buɗaɗɗen shugabanci, wanda ya haifar da haɗin kai da kwanciyar hankali a tsakanin malamai, ɗalibai da ma’aikata. Haka kuma, ta yaba da kokarinsa na tabbatar da ingantaccen ilimi mai dacewa da ƙalubalen zamani.
Baya ga rawar da ya taka a jami’ar, sanarwar ta bayyana Farfesa Pate a matsayin fitaccen masani a fannin sadarwa, wanda gudunmawarsa ta taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban nazarin sadarwa da aikin jarida a Najeriya. Tasirinsa, a cewar Majalisar, na ci gaba da zaburar da sabbin masana da kwararru a fagen.
NUJ ta kuma yaba da kyakkyawar dangantaka da hadin gwiwar da ya ƙarfafa tsakanin jami’ar da kafafen yaɗa labarai, tana mai cewa fahimtarsa game da muhimmancin aikin jarida wajen gina kasa ta samar da mutunta juna da kyakkyawar fahimta tsakanin bangarorin biyu.
Yayin da Farfesa Pate ke miƙa ragamar shugabanci, Majalisar ta bayyana kwarin gwiwar cewa kwarewarsa da gogewarsa za su ci gaba da amfani ga kasa a wasu manyan mukamai na kasa da kasa.
Haka zalika, Majalisar ta yi kira ga sabon Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Muhammad Inuwa Ja’afaru, da ya ci gaba da gina kan nasarorin da aka samu, tare da koyi da nagartaccen jagoranci, tawali’u da hangen nesa da magabacinsa ya nuna.
A ƙarshe, Majalisar NUJ ta Jihar Gombe ta yi wa Farfesa Umaru A. Pate fatan alheri da karin nasarori a dukkanin ayyukansa na gaba, tana mai cewa gudunmawarsa za ta ci gaba da zama ginshiki wajen bunkasa ilimi da ci gaban kasa.

