Wata Kotu a Kano ta tura jarumar Kannywood gidan yari na tsawon watanni shida

 


Babban Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a S.M Shuaibu, ta yanke wa jarumar Kannywood, Saadatu Mohammed Inuwa (wacce aka fi sani da Samha), hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni shida a yau Juma’a, 13 ga Fabrairu, 2026, saboda laifin wulaƙanta takardar kuɗin Naira.

Hukumar ta gurfanar da jarumar ne a kan tuhuma guda ɗaya da ta shafi lalata kuɗin ƙasar Najeriya, wanda hakan ya saɓa wa tanadin dokar Babban Bankin Najeriya (CBN) ta shekarar 2007.

Tuhumar da aka yi wa jarumar ta nuna cewa: "Ke Saadatu Mohammed Inuwa, a wani lokaci a shekarar 2022, a ƙarƙashin ikon wannan kotu, kin lalata takardar Naira dubu ɗaya (N1,000) da Babban Bankin Najeriya ya fitar ta hanyar goge hancinki da ita, wanda hakan ya zama laifi akasin sashi na 21 (1) na dokar CBN ta shekarar 2007."

Samha ta amsa laifinta sa’ilin da aka karanta mata tuhumar. Bayan amsa laifin, lauyan mai ƙara, Musa Isah, ya bayyana hujjojin shari’ar sannan ya buƙaci kotun da ta yanke mata hukunci da ya dace.

Jarumar ta roƙi kotun da ta yi mata sassauci, inda ta bayyana cewa wannan ne karon farko da ta taɓa aikata laifi kuma tana nadamar abin da ta yi.

Daga ƙarshe, Mai Shari’a Shuaibu ya yanke wa Inuwa hukuncin zaman gidan yari na watanni shida (6), tare da zaɓin biyan tara ta kuɗi naira dubu ɗari biyu (N200,000) kawai.