Sanatocin Kano da Ebonyi sun yi musayar yawu


An samu takaddama tsakanin Mataimakin Shugaban Whip na Majalisar Dattawa, Sanata Peter Nwaebonyi (APC, Ebonyi North), da Mataimakin Whip na ‘yan adawa, Sanata Rufai Hanga (NNPP, Kano Central), yayin zaman kare kasafin kuɗin Ma’aikatar Ayyuka.



Zaman, wanda Sanata Hanga ya jagoranta a matsayin mataimakin shugaban kwamitin, ya rikide zuwa ce-ce-ku-ce bayan ya nemi Nwaebonyi ya taƙaita jawabinsa. Nwaebonyi ya nuna rashin jin daɗi, yana mai cewa ba za a hana shi magana ba bayan an bai wa wasu sanatoci damar yin jawabi na tsawon lokaci.


Hanga ya buge teburin shugabanci tare da umartar Nwaebonyi ya dakatar da magana, lamarin da ya ƙara tsananta musayar kalamai a tsakaninsu. Daga bisani dai wasu sanatoci suka shiga tsakani, inda aka dawo da zaman cikin natsuwa.


A yayin zaman, Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, ya ƙalubalanci kwamitin da su je su duba aikin titin Abuja–Kaduna–Zaria–Kano, yana mai cewa zai yi murabus idan aka tabbatar aikin bai kai ƙa’ida ba. Ya kuma bayyana cewa daga cikin kasafin Naira tiriliyan 3.245 na ma’aikatar a 2026, Naira biliyan 760 za a ware su ga sabbin ayyuka a faɗin ƙasar.