SAI KASIYAR DA KWANON MASARA HUDU ZAKA SAYI JAKAR MAGI

Sai Talaka Ya Siyar Da Kwanon Masara Hudu shine Zai Iya Siyan Ledar Magi daya kacal Daga Ahmad Hussain Ahmad Tabbas talakawa zasu kara talaucewa masu kudi zasu kara tara kudi domin sune masu ma'aikatu kuma sune diloli masu siyarwa da talakawa kuma duk sune masu karawa kaya kudi. Domin wannan karyewar kayan masarufin da sauran kayayyakin akan talaka zata kare. Wallahi muna fata kuma muna son kowane irin kaya yayi arha tun daga kan na ma'aikatu, kayan abinci da sauran kayayyakin komai yayi sauki, amma bamu son adadin kayayyakin talakawa ne kadai zai karye. A yanzu haka wasu wajajen ana sayar da buhun masara dubu 13 karamin kwano 170, sai talaka ya saida kwanan masara Hudu kafin ya sayi ledar Magi guda daya kacal. Matukar iya kayayyakin talakawa ne da suke dan sayarwa wasu a shaguna wasu a karkara wasu a cikin gidajensu suka karye suka tafka asara na tabbata talakawa da dama zasu kara talaucewa fiye da yadda suke a yanzu. Wallahi duk wanda ya kasa kayanshi a kasuwanni babu masu siya kuma bashida kudin Cefane dole ya karyar da kayan shi ya sayar asara domin ya samu kudin da zai kai gida a yi amfani dasu. Da yawan mutane jarinsu zai karye a wannan lokacin matukar ba'a samu chanji ba.