KANO, NAJERIYA – Cikin yanayi na alhini da juyayi, Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, a yau Laraba ya kai ziyarar ta’aziyya ta musamman zuwa gidan Malam Haruna Bashir da ke unguwar Ɗorayi Chiranci, wanda wasu miyagu suka kashe wa mata da yara guda shida.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya ziyarci gidan tare da wasu manyan jami’an gwamnatinsa, ya tattauna da Malam Haruna cikin nuna juyayi, inda ya bayyana cewa wannan rashin ba na Malam Haruna ba ne kawai, rashi ne da ya taɓa zuciyar kowane ɗan jihar Kano.
Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta huta ba har sai an kamo waɗanda suka aikata wannan danyen aikin an kuma hukunta su.
A matsayin hanyar tallafi da sanyaya zuciyar mahaifin da aka zalunta, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da ba wa Malam Haruna Bashir kyautar kujerar aikin Hajji na shekarar 2026.
Gwamnan ya bayyana cewa wannan dama ce da za ta ba Malam Haruna sararin gudanar da ibada da addu’o’i a ƙasa mai tsarki domin neman sauƙin wannan babban rashi da ya samu.
Malam Haruna Bashir ya nuna matuƙar godiyarsa ga Gwamnan bisa wannan ziyara da kulawa da ya nuna masa a daidai lokacin da yake cikin mafi munin yanayi a rayuwarsa.
Al'ummar unguwar ta Chiranci da sauran jama'ar jihar Kano da suka shaida wannan ziyara sun jinjina wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa nuna damuwarsa kai-tsaye ga halin da talakawa ke ciki, musamman a wannan lokaci na jarrabawa.
