Daga Wakilinmu, Kano
Rundunar yan sandan Jihar Kano ta sanar da samun gagarumar nasara wajen fatattakar miyagu, inda ta yi nasarar cafke wani hatsabibin ɗan daba da ya daɗe yana addabar mazauna birnin Kano.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a madadin Kwamishinan Yan Sanda, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cewa an kama matashin ne mai suna Auwalu Ali, wanda aka fi sani da ‘Auwalu Ɗan Daba’, ɗan shekara 26, a ranar 31 ga watan Janairu, 2026. Rundunar ta bayyana cewa an kama Auwalu ne a unguwar Dorayi bayan samun sahihan bayanan sirri kan yadda yake jagorantar ƙungiyoyin yan daba wajen kai wa jama’a hari da ƙwace musu dukiya.
A wani labari mai nuna kishin ƙasa da tausayi, rundunar ta bayyana yadda jami'anta na ofishin Sharada suka amsa kiran gaggawa bayan an kama wani da ake zargin ɗan fashi ne wanda ya raunata wata mata. Bayan garzaya da matar zuwa asibitin Murtala Mohammed domin ceto ranta, wani jami’in ɗan sanda ya nuna bajinta inda ya sadaukar da jininsa (blood donation) domin ceton rayuwar matar.
Kwamishinan yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya jinjina wa jami’an bisa wannan sadaukarwa, musamman jami’in da ya bayar da jininsa, yana mai jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da ba da kariya ga rayuka da dukiyoyin al’umma. Haka kuma ya gode wa mutanen jihar bisa haɗin kan da suke ba wa hukumar.
Rundunar ta buƙaci al’umma da su kasance masu faɗakarwa tare da kai rahoton duk wani motsi na shakku zuwa ofishin yan sanda mafi kusa, ko kuma kira ta lambobin gaggawa kamar haka: 08032419754, 08123821575, ko 09029292926.
