Yayin taron, Shugaba Tinubu ya bayyana kudurinsa na daidaita tattalin arziki da inganta rayuwar al'umma ta hanyar zuba jari a fannin ilimi da more rayuwa. Shi ma a nasa bangaren, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana cewa Jihar Gombe tana sahun gaba wajen marawa wadannan kudurori baya ta hanyar sauya fasalin fannin noma, ilimi, da masana'antu.
Gwamnan ya jaddada cewa Jihar Gombe ta zama zakaran gwajin dafi a Arewa Maso Gabas wajen samar da ayyukan yi da wadatar abinci, sannan ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki kafada-da-kafada da gwamnatin tarayya domin samar wa talaka romon damokradiyya.


