KANO, Najeriya — Hukumar Shari’a ta jihar Kano ta fitar da gargaɗi mai tsauri ga masallatan Juma’a da su daina rufe hanyoyin mota yayin gudanar da salla, inda ta yi barazanar gurfanar da duk masallacin da ya saba wannan umarni a gaban kotu.
Shugaban hukumar, Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 5 ga watan Fabrairu, 2026, yayin taron majalisar zartarwa na hukumar da aka gudanar don tattauna hanyoyin kyautata jin daɗin al’ummar jihar.
Wannan mataki ya zo ne dai-dai lokacin da shugabannin hukumar ke cika shekara guda cif da fara aiki, tun bayan rantsar da su da Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi.
Kwamishina na biyu a hukumar, Sheikh Ali Ɗan Abba, ya ƙara tabbatar da cewa zaman nasu ya mayar da hankali ne kan abubuwan da za su kawo ci gaba da kuma sauƙaƙa wa jama'a zirga-zirga a faɗin jihar.
A ƙarshe, Sheikh Abbas Daneji ya sake nanata kira ga masu rufe hanyoyi da su gaggauta daina hakan domin guje wa fuskantar hukunci, yana mai jaddada cewa an riga an tanadi dokokin da za su yi aiki a kan duk masallacin da ya yi kunnen ƙashi.
