Gwamna Abba Kabir Ya Tallafa wa Wadanda Gobara Ta Shafa a Kasuwar Singer Da N100m

 

Hoto: Sanusi Bature Dawakin Tofa 

KANO, Najeriya — Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanar da bayar da tallafin naira miliyan 100 ga ’yan kasuwar Singer da gobarar daren jiya ta shafa, a matsayin tallafin gaggawa na rage radadin asarar da suka tafka.

Hoto: Sanusi Bature Dawakin Tofa 


Gwamnan ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis yayin da ya kai ziyarar gani da ido tare da jajantawa shugabannin kasuwar da ’yan kasuwar da lamarin ya ritsa da su.

Cikin wata sanarwa da babban mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanya wa hannu, Gwamna Yusuf ya bayyana matukar damuwarsa kan yawaitar gobara a kasuwannin jihar, inda ya tabbatar da aniyar gwamnatinsa na samar da matakan kariya na din-din-din.

Zamanantar da Kasuwanni da Gyaran Hanyoyi A yayin ziyarar, Gwamnan ya kuma kaddamar da katafaren aikin gyara da fadada hanyoyin mota da suka hada da Bello Road, Ado Bayero Road, Kandoki, Yolawa, da Kwangiri, wanda aka kiyasta zai lakume naira biliyan uku (N3bn).

"Wannan aiki na da nufin magance cunkoson ababen hawa da kuma kawo karshen matsalar ambaliyar ruwa da ke addabar yankunan kasuwanninmu," in ji sanarwar.

Gwamna Yusuf ya bai wa ’yan kwangilar da aka damka wa aikin wa’adin kwanaki 10 su koma bakin aiki, sannan ya yi alkawarin sanya wutar lantarki ta hasken rana (Solar) a cikin kasuwar domin zamanantar da harkokin kasuwanci da kuma kara inganta tsaro.

Hoto: Sanusi Bature Dawakin Tofa 

Godiya daga Shugabannin Kasuwa A nasu bangaren, shugabannin kasuwar Singer karkashin Barr. Junaidu Muhammad Zakari da dattawan kasuwar, sun gode wa gwamnan bisa wannan dauki, inda suka bayyana shi a matsayin wanda ya zo a daidai lokacin da suke cikin matsananciyar bukata.

Wannan ziyara dai na zuwa ne a yayin da gwamnatin jihar ke ci gaba da kokarin sabunta birnin Kano karkashin tsarin nan na "Urban Renewal" domin bunkasa tattalin arzikin jihar.