BAUCHI, Najeriya — Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed (CON), ya kai ziyarar jaje a asibitin koyarwa na Sir Abubakar Tafawa Balewa, domin duba halin da ’yan jaridar da suka yi hatsari kwanan nan suke ciki.
Kamar yadda wakiliyar Fidelity Hausa, Habiba Ahmad Diyee ta ruwaito, Gwamnan ya zagaya dukkan ɗakunan da ma'aikatan yaɗa labaran suke kwance, inda ya jajanta musu tare da yi musu addu'ar samun sauƙi cikin gaggawa.
Yayin ziyarar, Gwamna Bala ya nuna matuƙar damuwarsa kan faruwar wannan hatsari. Domin rage wa iyalansu raɗaɗi, Gwamnan ya ba da umarni ga mahukuntan asibitin cewa gwamnatin jiha ta ɗauki nauyin jinyar dukkan ’yan jaridar tun daga yanzu har zuwa lokacin da za su samu lafiya su fito.
Haka zalika, Gwamnan ya jinjina wa likitoci da ma'aikatan jinya na asibitin bisa namijin ƙoƙarin da suke yi wajen kula da marasa lafiyan, inda ya kammala da addu'ar Allah ya tsare aukuwar hakan a nan gaba.
